28 Satumba 2020 - 11:04
Bahrain: An Kama Wani Malamin Addini Saboda Sabawa Shirin Gwamnati Na Maida Hulda Da Isara’ila

Jami’an tsaro a kasar Bahrain sun kama wani malamin addini saboda wasu shirye-sgityen da yake gabatarwa wadanda suka sabawa shirin gwamnatin kasar na maida cikekken huldar jakadanci da Haramtacciyar kasar Isra’ila.

ABNA24 : Har’ila yau labarin ya kara da cewa jami’an tsaron sun kama wasu matasa guda biyu a birnin Manama babban birnin kasar da kuma yankin Siba saboda shiga cikin wata zanga-zangar yin allawadai da maida hulda da HKI wanda gwamnatin kasar ta yi.

Banda haka Jami’an tsaron sun kama Abdul-Husain Ahmad wani matashi mai tsara wakoki wanda ya tsara wake wacce a cikinta yake sukar gwamnatin kasar dangane da maida hulda da HKI.

A ranar 25 ga watan Augustan da ya gabata ne kasashen Bahrai da UAE suka maida cikekken Hulda da HKI a wani bikin da aka gudanar tare da shugaban kasar Amurka Donal Trump a birnin Washington.

342/